Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Kulen Allah na ƙasa, ya kai ziyara ofishin Jaridar Neptune da ke Abuja

0
286

Shugaban ƙungiyar Makiyaya ta Kulen Allah na ƙasa (KACRAN), Hon. Khalil Muh’d Bello, ya kai ziyarar ban girma a Ofishin Jaridar Neptune Prime da ke Abuja, domin ya nuna jin daɗin ‘ya’yan ƙungiyar a game da namijin ƙoƙarin da kafar yaɗa labaren ke yi ba dare ba rana, da zummar wayar da kan ‘yan Najeriya a kan muhimmancin zaman lafiya da hakuri da juna.

A yayin ziyarar, Hon. Bello ya yabawa Neptune Prime bisa aikin da suke yi na wayar da kan ƴan ƙasa akan zaman lafiya, sannan ya buƙaci kafafen yaɗa labarai da su ci gaba da ƙoƙarin haɗa kan ‘yan Najeriya.

Bugu da ƙari, shugaban na KACRAN ya yi ƙira ga gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohin Arewa da su bi sahun gwamnan jihar Yobe, Hon. Mai Mala Buni, wajen tallafawa makiyayan jihohinsu ta hanyar samar musu da abuhuwan jin daɗin mulkin dimukuraɗiya.

KU KUMA KARANTA: Kwamishinan yaɗa labaran jihar Yobe, Bego, ya ziyarci babban ofishin jaridar Neptune Prime a Abuja

Har ila yau, a cikin jawabinsa, Hon. Bello ya yabawa gwamna Mai Mala Buni bisa yadda ya gaggauta ɗaukar matakin magance matsalolin makiyayan Jiharsa, da yadda ya raba kayan tallafi ga al’ummar makiyayan Jiharsa ta Yobe, inda ya buƙaci sauran gwamnonin Jihohin Arewa da su yi ƙoƙari wajen taimakawa makiyaya ta fannin raba kayan tallafi.

Shugaban na KACRAN ya kuma nuna matukar farin ciki da alfaharin yin haɗin gwiwa da Neptune Prime domin bayar da gudunmawa ga ci gaban ƙasa da samar da zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya.

Mawallafin jaridar Neptune Prime, Dr Hassan tare da Shugaban KACRAN Hon. Khalil.

A yayin da yake maida jawabi, Mawallafin gidan Jaridar ta Neptune Prime, Dr Hassan Gimba ya godewa Hon. Khalil Muh’d Bello a saboda wannan muhimmiyar ziyara ta tarihi da ya kaiwa kamfanin Jaridar ta Neptune Prime, tare da ba da tabbacin kamfanin wajen ci gaba da haɗa kan kafofin yaɗa labarai na ƙasa na ganin an haɗa kan ‘yan Najeriya ta hanyar ci gaba da watsa labarai masu sahihanci da za su ƙara haɗin kan ‘yan ƙasa.

Leave a Reply