Shugaban ’yansandan Mopol na Legas ya Musulunta a Kano
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da ya yi fice wajen kwatanta gaskiya da amana, ACP Daniel Amah, ya karɓi Addinin Musulunci a Fadar Sarkin Kano.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ne, ya jagoranci musuluntar da shi tare da sanya masa sabon suna, Muhammadu Sanusi.
Sarkin ya yi ƙira ga Muhammad Sanusi da ya zurfafa iliminsa na addinin Musulunci, ciki har da koyon yadda ake sallah, azumi, da bayar da zakkah.
Haka kuma, ya shawarce shi da ya ci gaba da girmama iyayensa, duk da bambancin addininsu, tare da riƙe kyawawan halayensa.
Sunan Mista Amah, ya yi amo a watan Afrilun 2022 bayan ya ƙi karɓar cin hancin dalar Amurka 200,000 da wasu ’yan fashi suka ba shi.
‘Yan fashin sun sato kuɗi sama da Naira miliyan 300, amma daga bisani suka shiga komarsa.
KU KUMA KARANTA: Yan sanda sun kama wani da ya caka wa ’yar shekara 8 almakashi a gabanta
Wannan hali nasa na riƙon gaskiya ya sa aka ɗaga darajarsa zuwa Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda a watan Nuwamban 2022.
Da yake magana kan dalilin da ya sa ya karɓi Addinin Musulunci, Muhammad Sanusi ya bayyana godiyarsa bisa kyakkyawar tarba da ya samu kuma ya yi alƙawarin neman ilimin addini tare da ci gaba da yi wa al’umma hidima.