Shugaban Tinubu ya rattaba hannu kan dokar Haraji

0
126
Shugaban Tinubu ya rattaba hannu kan dokar Haraji

Shugaban Tinubu ya rattaba hannu kan dokar Haraji

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya sanya hannu kan dokokin gyaran haraji guda huɗu da suka samu amincewar majalisun dokoki na tarayya, a wani mataki da ake ganin zai sauya tsarin haraji da tattalin arzikin ƙasar gaba ɗaya.

KU KUMA KARANTA:Majalisar wakilai a Najeriya, ta amince da ƙudirin dokar haraji a ƙasar

Bikin sanya hannun ya samu halartar shugaban majalisar dattawa, kakakin majalisar wakilai, shugabannin kwamitocin kudi na majalisu, shugaban kungiyar gwamnoni, ministan kudi da kuma babban lauya na ƙasa.

Dokokin da aka sanyawa hannu sun haɗa da Kudurin Dokar Haraji na Najeriya, Kudurin Dokar Gudanar da Haraji, Kudurin Kafa Hukumar Tara Haraji ta Najeriya, da Kudurin Kafa Hukumar Haɗin Gwiwar Tara Haraji.

Leave a Reply