No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban rundunar Sojin ƙasa Lagbaja bai mutu ba – Rundunar Sojin Najeriya

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rundunar Sojin Ƙasa ta Najeriya a ranar Lahadi ta ƙaryata raɗe-raɗin da ake yi cewa Shugaban Rundunar Sojin Ƙasa, COAS, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya mutu.

PRNigeria ta rawaito cewa rundunar, a shafin ta na X ta bayyana rahoton a matsayin ƙarya, amma ba ta ba da wani ƙarin bayani ba.

Sai dai kuma a wata sanarwa da Kakakin rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu ya fitar a ranar Asabar, Lagbaja ya tafi hutu ne da kuma duba lafiyar sa a ƙasar waje.

KU KUMA KARANTA: Ba mu da niyyar kafa sansanin soji a Najeriya – Amurka

Ya kuma nuna cewa babu wani giɓi na shugabanci a runudunar sakamakon tafiyar COAS ɗin, inda ya baiyana cewa tuni shugaban sashen manufofi da tsare-tsare na rundunar, Manjo-Janar Abdulsalami Bagudu Ibrahim ya maye gurbin sa kafin ya dawo.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...