Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karasuwa jihar Yobe Lawan Gana, ya rasu

Daga Ibraheem El-Tafseer

A yammacin ranar Alhamis ne, Allah ya yiwa shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karafuwa, Alhaji Lawan Gana rafuwa. Ya rasu ne sakamakon gajeruwar rashin lafiya.

Daraktar yaɗa labarai na gwamnan jihar Yobe, Alhaji Mamman Muhammad ne ya sanar da rasuwar Lawan Karasuwa a wajen taron wayar da kan jama’a da Kwamishinan Ma’aikatar Samar da Arziƙi, Ƙarfafawa da Samar da Aikin yi ta Jihar ta shirya.

Ya ce Gana ya rasu ne a Afibitin gwamnatin tarayya dake Nguru bayan gajeruwar rashin lafiya.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Nasarawa ya rasa ƙaninsa, watanni bayan rasuwar ɗansa

Gana kafin rasuwarsa, ya riƙe muƙamin shugaban ƙaramar hukumar Karasuwa na tsawon watanni shida kafin Gwamna Mai Mala Buni ya rushesu. Daga nan aka sake naɗa shi a matsayin shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karasuwa a karo na biyu.

Yana ɗaya daga cikin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 17 da za a rantsar gobe Juma’a, shi kuma Allah ya masa rasuwa yau Alhamis.


Comments

One response to “Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karasuwa jihar Yobe Lawan Gana, ya rasu”

  1. […] KU KUMA KARANTA: Shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Karasuwa jihar Yobe Lawan Gana, ya rasu […]

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *