Shugaban majalisar Malamai ta ƙasar Saudiyya Sheikh Abdul’aziz Bin Abdullah Bin Al-shekh ya rasu
Daga Jameel Lawan Yakasai
Hukumomin ƙasar Saudiyya sun sanar da rasuwar Shugaban Majalisar malaman ƙasar Saudiyya Sheikh Abdulaziz Bin Abdullah Al-Sheikh mai shekaru 82 a ranar Talata.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya tarbi tagwayen da aka haifa a haɗe, bayan an yi aikin raba su a Saudiyya
An gabatar da jana’izarsa a Imam Turki Bin Abdullah a Riyadh bayan sallar La’asar a ranar Talata, kuma an umarci sallatul Gha’ib a masallacin Harami a Makkah da Masallacin Annabi (S.A.W) a Madinah da dukkan masallatan Saudiyya bayan sallar La’asar.
Allah ya yi masa gafara.









