Shugaban Kenya ya tuƙa kansa a cikin motar lantarki zuwa taron matasa

A ranar Lahadin da ta gabata ne shugaban ƙasar William Ruto ya tuƙa kansa a cikin wata mota mai amfani da wutar lantarki zuwa cibiyar taron ƙasa da ƙasa ta Kenyatta da ke KICC.

KICC ce za ta kasance wurin da za a gudanar da taron ƙoli kan yanayi na Afirka wanda za a gudanar daga ranar Litinin 4 zuwa 6 ga Satumba.

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa ta yanar gizo, an ga shugaban yana tuƙa mota mai rawaya daga fadar gwamnati zuwa KICC.

Ya samu rakiyar wata ayarin motocin lantarki masu amfani da wutar lantarki da suka haɗa da masu tuƙa babura biyu, motoci biyu da kekunan lantarki guda biyu.

Shugaban ya ziyarci KICC ne domin halartar taron sauyin yanayi na matasan Afirka, wanda shi ne mafarin taron ɗumamar yanayi na Afirka da za a fara ranar Litinin mai zuwa.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Nijar sun amince su tattauna da ECOWAS

Taron ƙolin kan sauyin yanayi na Afirka zai yi daidai da makon yanayi na Afirka wanda zai gudana daga ranar 4 zuwa 8 ga watan Satumba.

Sama da wakilai 30,000 ne ake sa ran za su halarci taron da suka haɗa da shugabannin ƙasashe da gwamnatoci sama da 25.

Yayin buɗe taron sauyin yanayi na matasan Afirka a ranar Asabar, Ruto ya yi ƙira ga matasan da su haɗa kai su shiga cikin taron.

Ya ce shaida haziƙan matasa masu hankali daga ko’ina cikin nahiyar suna baje kolin hanyoyin magance yanayi yana ba shi farin ciki matuƙa.

“Watanni biyu da suka gabata, a ƙarƙashin Hasumiyar Eiffel, na yi ƙira ga matasan duniya da su zo tare da mu a Nairobi don zaɓar yanayin duniya,” in ji shi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *