Shugaban KAROTA ya bada umarnin tsare wasu jami’insa kan badaƙala

0
218

Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta ce ya zama wajibi ta ɗauki matakin fitar da ɓata-garin cikinta domin inganta ayyukan hukumar.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Hukumar Karota Engr. Faisal Mahmud Kabir ne ya bayyana haka a wannan rana ta Alhamis lokacin da ya bayar da umarnin tsare wasu Jami’in KAROTA waɗanda ake zargi su da matsawa direbobin mota da karɓe-karɓen kuɗi a wajen su.

Yace hukumar baza ta zuba ido ta bari a sauke tsarin da aka kafa hukumar a kai ba, a don haka ya zama wajibi a hukunta duk wanda aka samu da sauya salon aikin hukumar.

KU KUMA KARANTA: Hukumar KAROTA ta cafke wasu matasa da tarin kayan maye da makamai a Kano

Yaja hankalin direbobin mota da su guji bawa jami’in hukumar ta KAROTA cin-hanci domin baya daga cikin manufar kafa Hukumar.

Ya kuma ƙara da cewa abinda ake buƙata a wajen kowanne direba ya shi ne tabbatar ya mallaki dukkan takardun tuƙi kafin ya hau kan titi, da kuma bin dokokin hanya a lokacin da ake tuƙin.

Daga karshe shugaban ya godewa wasu daga cikin Jami’in Hukumar bisa namijin kokarin da suke yi wajen aiki tukuru tare da tsare mutuncin ayyukan Hukumar.

Leave a Reply