Shugaban kamfanin Suzuki, ya mutu yana da shekaru 94
A ƙarƙashin jagorancin ɗan kasuwar mai kwarjini na tsawon shekaru 40 har zuwa 2021, yawan cinikin kamfanin ya ruɓanya har sau 10.
Osamu Suzuki, wanda ya bunƙasa ƙaramin kamfanin da ya shahara wajen ƙirar motoci zuwa kamfanin ƙasa da ƙasa da ya samu ɗimbim nasarori a kasar Indiya, ya mutu a Larabar da ta gabata yana da shekaru 94 bayan ya sha fama da cutar sankara, kamar yadda kamfanin ya bayyana a yau Juma’a.
A karkashin jagorancin dan kasuwar mai kwarjini na tsawon shekaru 40 har zuwa 2021, yawan cinikin kamfanin ya rubanya har sau 10.
KU KUMA KARANTA:Burkina Faso ta dakatar da ƙarin wasu kafafen watsa labarai na Ƙasashen Yamma
Osuma wanda aka haifa a ranar 30 ga watan Janairun 1930, a yankin Gifu dake tsakiyar kasar Japan, ya yi aure cikin iyalan mutanen da suka assasa kamfanin kafin daga bisani ya zamo shugabansa a 1978.
Ya maida hankalinsa wajen kerar ababen hawan “Kei” marasa nauyi, wadanda galibinsu suka yi shura saboda karancin shan mai da saukin sarrafawarsu
Ya kuma yi kokari wajen neman yin hadin gwiwa da kamfanonin kasa da kasa da damammaki a kasashen ketare domin fadada kasuwancinsa.
Kamfanin kirar motocin ya taba kulla alaka da kamfanonin GM da Volkswagen sannan ya shiga kawancen hannun jari da kamfanin Toyota a shekarar 2019.