Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerarsa 

0
183
Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerarsa 
Mahmud Yakubu, tsohon shugaban INEC

Shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa INEC Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerarsa

Farfesa Mahmood Yakubu ya sauka daga kujerar Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

Yakubu, wanda aka nada a shekarar 2015, ya yi wa’adin shekaru biyar sau biyu a ofis.

A ranar Talata, ya mika ragamar shugabanci ga May Agbamuche, kwamishina a hukumar, wacce za ta rike mukamin a matsayin mai rikon kwarya.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan Najeriya fiye da miliyan 6.2 sun kammala matakin farko na rajistar katin zaɓe ta yanar gizo – INEC

Tsohon shugaban hukumar ya roƙi tsofaffin abokan aikinsa da su ba wa mai rikon kwaryar cikakken hadin kai har zuwa lokacin da za a nada sabon shugaban hukuma na dindindin.

Ana sa ran Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanar da sabon shugaban hukumar zabe a kowanne lokaci daga yanzu.

Leave a Reply