Shugaban hukumar zaɓen Bauchi Ahmed Makama ya rasu

0
253
Shugaban hukumar zaɓen Bauchi Ahmed Makama ya rasu
Marigayi Alhaji Ahmed Makama

Shugaban hukumar zaɓen Bauchi Ahmed Makama ya rasu

Daga Shafaatu Dauda Kano

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Bauchi (BASIEC), Alhaji Ahmed Makama Hardawa, ya rasu.

A wata sanarwa da mai ba Gwamnan Jihar Bauchi shawara kan harkokin yada labarai, Mukhtar Gidado, ya fitar a ranar Laraba 30 ga Yuli, Gwamna Bala Mohammed ya bayyana bakin cikinsa kan rasa wannan jigo mai daraja.

Sanarwar ta bayyana cewa marigayin ya rasu ne a ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025, a birnin Abuja, bayan gajeruwar rashin lafiya.

Gidado ya ce, “Marigayi Alhaji Ahmed Makama Hardawa ya kasance jigo a harkokin gwamnati, hazikin jami’i, kuma dan kasa mai kishin kasa, wanda ayyukansa na gaskiya da rikon amana suka bar tarihi a Bauchi da Najeriya baki daya.

“Ya taba rike mukamin Kwamishinan Zabe na Kasa (REC) a jihohin Taraba da Nasarawa, inda ya gudanar da aikinsa cikin gaskiya, rikon amana, da adalci – halayen da suka kasance ginshikin rayuwarsa.”

A matsayinsa na shugaban BASIEC, Hardawa ya taka muhimmiyar rawa wajen karfafa dimokuradiyya a matakin kananan hukumomi ta hanyar tabbatar da tsarin zabe mai gaskiya da sahihanci.

KU KUMA KARANTA: Arewacin Najeriya zai bayyana matsayarsa kan zaɓen 2027 – Hakeem Baba-Ahmed

Girmamawarsa ga doka da ci gaban hukumomi ya sa aka girmama shi daga abokan aiki, ‘yan siyasa, da al’umma gaba daya,” in ji sanarwar.

Gwamna Bala Mohammed ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai basira, tawali’u, da nagartaccen shugabanci, wanda za a yi matukar rashin jajircewarsa a wannan lokaci na kalubale a tafiyar da dimokuradiyya.

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, hukumar BASIEC, abokai da ‘yan uwa, da daukacin al’ummar Hardawa da Masarautar Misau.

Ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta masa kurakuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, kuma Ya bai wa danginsa hakurin jure wannan babban rashi.

Rahotanni sun nuna cewa za a gudanar da sallar jana’izar marigayin a yau Laraba, 30 ga Yuli, 2025, da karfe 5:00 na yamma a fadar mai martaba Sarkin Bauchi.

Leave a Reply