Shugaban hukumar tsaro ya ajiye aiki kan zargin alaƙa da ‘yan bindiga daga naɗa shi

0
219

Jim kaɗan bayan rantsar da shi a matsayin shugaban kwamitin da zai kafa jami’an tsaron sa kai, Garba Moyi Isa ya yi murabus.

Rahoto ya zo daga Leadership cewa Kanal Garba Moyi Isa mai ritaya ya sauƙa daga kujerar da gwamnatin jihar Sakkwato ta nemi ɗaura shi.

Garba Moyi Isa ya yi murabus ne bayan ‘yan awanni da rantsar da kwamitinsa mai mutum 25 a yunƙurin an kawo zaman lafiya a Sakkwato.

Ana tunani tsohon sojan ya ɗauki wannan mataki ne saboda wani bidiyo da aka fitar, ana zargin ya na da alaƙa da ‘yan ta’addan da ke Sakkwato.

Garba Moyi wanda ya riƙe kujerar Kwamishina har sau uku a jihar Sokoto, ya tara manema labarai a ƙarshen makon jiya, ya yi jawabi.

KU KUMA KARANTA: Za mu inganta tsaro ta hanyar haɗa kan jami’an tsaro da tattara bayanan sirri

Tsohon jami’in tsaron ya yi bayanin yadda ya bautawa ƙasarsa na shekara da shekaru a gidan soja, daga baya kuma ya shigo siyasa.

Ko a rahoton da aka samu daga jaridar Punch, haka dai aka ji cewa Moyi bai ba da asalin abin da ya jawo ya ajiye kujerar da aka ba shi ba.

Leave a Reply