No menu items!

Sample Page Title

Date:

Shugaban hukumar tattara bayanan sirri na ƙasa ya yi murabus

Shugaban Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA), Ahmed Rufai Abubakar, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Ya bayyana haka ne ga maneman a fadar shugaban ƙasa, jim kaɗan bayan ganawarsa da shugaba Tinubu.
Ya gode wa shugaba Tinubu bisa ba shi damar ci gaba da jagorantar hukumar bayan ya zama shugaban ƙasa.

Ya ce, ya je fadar shugaban ƙasar ne domin ganawa da shi, don yi masa bayanai kamar yadda ya saba a ko yaushe, wanda daga nan ne ya ajiye aikinsa.

“Bayan na yi masa jawabi, na kuma gabatar masa da takardar ajiye aikina, kuma shugaban ƙasar ya karɓe ta tare da amincewa da ita.

KU KUMA KARANTA:Shugaban hukumar leƙen asirin sojin Isra’ila ya yi murabus saboda harin Hamas na 7 ga Oktoba      

“Na gode masa bisa damar sa ya ba ni na yi wa Najeriya hidima, kuma ya ƙara tsawaita lokacin zuwa watanni 15…”

To sai dai bai yi cikakken bayani kan dalilinsa na ajiye aikin a daidai wannan lokacin ba.

Ya kuma ce yana alfahari bisa aikin da ya yi da shugabannin ƙasar har guda biyu.

A watan Janairun 2018 ne dai tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar, bayan korar tsohon shugaban hukumar Ayo Oke, bisa zargin almundahana.

Tsohon mai shekara 71, ya yi ritaya daga aiki a Jihar Katsina, tare da shiga sashen tsaro na ma’aikatar harkokin wajen Najeriya a 1993.

A shekarar 2015, an naɗa shi babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa (SSAP) kan hulɗa da ƙasashen duniya da kuma harkokin waje.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...