Shugaban hukumar leƙen asirin sojin Isra’ila ya yi murabus saboda harin Hamas na 7 ga Oktoba      

0
171

Rundunar sojojin Isra’ila ta ce shugaban hukumar leƙen asirinta ya yi murabus saboda gazawarsa wajen hana harin ba- zata da ƙungiyar Hamas ta kai ƙasar a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya ƙeta kariyar tsaron Isra’ila.

Aharon Haliva, shugaban hukumar leken asirin sojin Isra’ila, ya zama jigo na farko a Isra’ila da ya sauka daga mukaminsa a ranar Litinin, bayan harin, wanda Isra’ila ta yi ikirarin kashe mutane 1,200, tare da yin garkuwa da wasu kusan mutane 250.

“Manjo Janar Aharon Haliva, tare da goyon bayan babban hafsan hafsoshin sojin kasar, ya bukaci ya yi murabus, biyo bayan alhakin da ya rataya a wuyansa a matsayinsa na shugaban hukumar leken asiri kan abubuwan da suka faru a ranar 7 ga watan Oktoba,” a cewar rundunar sojin Isra’ila.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe ƙarin gomman Falasɗinawa a sabbin hare-haren da ta kai Gaza

“An yanke shawarar cewa Manjo Janar Aharon Haliva zai ajiye mukaminsa kuma zai yi ritaya daga rundunar leƙen asirin sojin Isra’ila IDF, da zarar an naɗa magajinsa cikin tsari da ƙwarewa.”

A takardar ajiye aikinsa, Haliva ya dauki alhakin gaza daƙile ko hana harin.

“A ranar Asabar, 7 ga Oktoba, 2023, Hamas ta kai wani mummunan harin ba-zata a kan Isra’ila,” kamar yadda ya rubuta a cikin wasikar da aka rundunar ta raba wa ƴan jarida.

“Sashen rundunar leken asirin da ke karkashin ikona ba su sauke nauyin da aka dora mana ba… tun daga nan nake dauke da wannan bakar rana a tare da ni, dare da rana, kuma zan ci gaba da rike kunciin yakin a raina.”

A wata sanarwa da rundunar sojin Isra’ila ta fitar ta ce babban hafsan sojojin kasar ya amince da bukatar Jaliva na yin murabus tare da gode masa bisa ga aikin da ya yi.

Ajiye aikin nasa na iya buɗe kofa ga wasu manyan jami’an tsaron Isra’ila su ɗauki laifin rashin dakile ko hana kai harin da kana su aije mukaminsu.

Leave a Reply