Shugaban hukumar KAROTA a Kano, ya buƙaci ma’aikatansa su ninka ƙoƙarin da suke yi don ƙara samar wa hukumar kuɗin shiga
Daga Shafaatu Dauda Kano
Hon. Faisal Mahmud ya yi wannan jawabi ne bayan wani taro da ya gudana tare da manyan jami’an hukumar, inda suka tattauna dabarun kara bunkasa hanyoyin samun kudaden shiga.
Ya bayyana cewa, kasancewar gwamnatin Abba Kabir Yusuf tana aiwatar da manyan ayyukan ci gaba a fadin jihar, ya zama dole hukumomin da ke da alhakin samar da kudaden shiga su ba da cikakken goyon baya ta hanyar kokarin kara kudin shiga da ake samu.
Ya tabbatar da cewa KAROTA za ta ci gaba da inganta walwalar ma’aikata domin samun karin kwazo da jajircewa.
A nasa bangaren, Daraktan Kudaden Shiga na KAROTA, Alhaji Nura Ahmad Diso, ya tabbatar wa shugaban KAROTA cewa za su sanya idanu sosai wajen sa ido a kan kudaden da ake tarawa domin rage asara da kuma hana salwanta.
KU KUMA KARANTA: KAROTA ta haramtawa manyan motoci hawa gadojin sama a Kano
Ya kuma dau alkawarin kara tsananta matakan sa ido da tabbatar da bin doka wajen tara kudade daga hanyoyin da suka hada da:
Takardun shiga tsakanin jihohi (Inter-state stickers).
Kudin jigilar kaya guda daya (Single Haulage Fee).
Kayan amfanin gona (Agricultural Produce).
Tashoshin manyan motoci (Trailers Park).
Taron ya hada da dukkan manyan jami’an hukumar KAROTA, jami’an hukumar karbar haraji ta cikin gida ta Kano da ke aiki tare da KAROTA, da kuma shugabannin sassan daban-daban na hukumar.









