Shugaban Guinea-Bissau ya ce yamutsin da aka yi a ƙasar ‘yunƙurin juyin mulki’ ne

0
194

Shugaban Guinea-Bissau Umaro Sissoco Embalo ya ce yamutsin da aka yi a babban birnin ƙasar tsakanin sojoji da Runduna ta Musamman da ke fadar shugaban ƙasa a ranar Alhamis wani “yunƙurin juyin mulki” ne.

Embalo, wanda ya je Dubai don halartar taron COP28 kan sauyin yanayi, ya ce ya kasa komawa ƙasarsa ne nan-take “saboda an yi yunkurin juyin mulki. Ina so na shaida muku cewa za a ɗauki mataki mai tsauri kan waɗanda suka haddasa wannan lamari”, in ji shugaban ƙasar yayin da ya koma Bissau ranar Asabar.

Rundunar sojin Guinea-Bissau ta umarci Dakaru na Musamman su koma bariki, bayan yamutsin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum biyu wanda ECOWAS ta yi Allah wadai da shi.

KU KUMA KARANTA: Yunƙurin Juyin Mulki: Ana musayar wuta a ƙasar Guinea

Ranar Alhamis da daddare rikici ya ɓarke tsakanin sojojin Dakaru na Musamman na Ƙasa da kuma Runduna ta Musamman da ke tsaron fadar shugaban ƙasa a Bissau babban birnin ƙasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum biyu.

Wani babban jami’in soji, wanda ba ya so a ambaci sunansa saboda sarƙaƙiyar lamarin, ya ce sojoji shida sun jikkata kuma an kai su makwabciyarsu Senegal.

Hankula sun kwanta ranar Juma’a da rana a ƙasar da ta yi kaurin suna wurin tashin hankali, bayan an bayar da sanarwa cewa sojoji sun kama Kanar Victor Tchongo, kwamandan Dakaru na Musamman na Ƙasar.

Ranar Asabar an rage yawan jami’an tsaro a kan titunan Bissau, amma an ga sojoji jibge a wasu wurare na musamman da suka haɗa da fadar shugaban ƙasa da ma’aikatar shari’a da wasu ma’aikatu.

Leave a Reply