Shugaban Ghana ya sallami Ministan Kuɗi, Ken Ofori-Atta, daga aiki

0
177

Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo ya cire ministan kuɗin ƙasar Ken Ofori-Atta daga mukaminsa, a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikinta.

Tun a shekarar 2017 Mista Oforri- Atta yake riƙe da muƙamin ministan kuɗi na Ghana, inda ya yi ta fuskantar suka kan taɓarɓarewar da tattalin arzikin ƙasar ke yi.

A shekarar 2022 matsalar ta daɗa ƙamari inda hauhawar farashin kayayyaki ta zarce kashi 50 cikin 100 sannan gwamnati ta gaza biyan lamuni.

Daga baya ta sake fasalin biyan bashinta da masu ba da lamuni don samun cancantar tallafin IMF.

A ranar Laraba ne aka naɗa Mohammed Amin Adam wanda ya taɓa riƙe muƙamin mataimakin ministan makamashi da kuma ƙaramin minista a ma’aikatar kuɗi a matsayin wanda ya maye gurbin Mista Ofori-Atta.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila za ta sallami wasu sojojinta na shirin ko-ta-kwana daga yaƙin Gaza

Ana sa ran Mista Adam zai sa ido kan shirin farfaɗo da tattalin arzikin na dala biliyan 3 daga IMF da ake ci gaba da yi da kuma batun sake fasalin basussukan masu ba da lamunin kasuwanci a ƙasar.

Shugaba Akufo-Addo ya maye gurbin wasu ministocinsa 12 a shirin sauya majalisar ministocin da aka yi ranar Laraba, gabanin zaɓen shugaban ƙasar Ghana da za a yi a watan Disamba shekarar 2024.

Leave a Reply