Shugaban Binance ya roƙi Gwamnatin Najeriya ta saki jami’insa da take tsare da shi

Shugaban kamfanin Binance, Richard Teng, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta saki ɗaya daga cikin manyan jami’an kamfanin da take tsare da shi.

Mista Teng ya bayyana haka ne a wani saƙo da kamfanin na Binance ya wallafa a shafinsa na intanet inda ya buƙaci gwamnatin ta saki Tigran Gambaryan domin ya tafi wurin iyalinsa.

Gwamnatin Najeriya ta kama Mista Gambaryan wanda shi ne shugaban kula da sashen laifukan kuɗi na Binance kan zargin halasta kuɗin haram inda kuma yake tsare a ƙasar sama da kwanaki 70.

An kama Gambaryan a watan Fabrairu bayan ya je ƙasar domin tattaunawa.

KU KUMA KARANTA: An gurfanar da jami’in Binance a gaban kotun Najeriya

A cikin sanarwar da shugaban na Binance ɗin ya fitar, ya ce kamfaninsa zai yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Najeriya domin tabbatar da cewa an warware matsalolin harajin da ake zargin ƙasar na bin kamfanin.

Shugaban na Binance ɗin ya bayyana cewa yana da muradin kamfaninsa ya yi aiki tare da Najeriya domin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasar.

A watan Maris, hukumar EFCC ta Nijeriya wadda ke yaƙi da rashawa ta zargi Binance da Gambaryan da abokin aikinsa Nadeem Anjarwalla da abubuwa da dama.

Daga ciki har da batun “aiki ba tare da lasisi ba, da cinikin kuɗin waje ba bisa ƙa’ida ba da ƙin biyan haraji da kuma ƙin bayyana asalin kuɗin shiga na dala miliyan 35.4.”

Sai dai tuni Nadeem Anjarwalla ya gudu daga Najeriya a lokacin da yake tsare a hannun jami’an tsaro, lamarin da ya yi matuƙar tayar da ƙura a Najeriya.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *