Hukumomi a Amurka da Najeriya, da kuma wasu masu faɗa a ji a Najeriya, sun tabbatar da mutuwar babban shugaban Bankin Access da iyalinsa.
Babban Shugaban bankin Access Bank, Herbert Wigwe, da matarsa, da kuma wani ɗansa sun mutu a wani hatsarin jirgin sama mai sauƙar ungulu daura da kan iyakar jahohin California da Nevada na Amurka. Jimlar mutane 6 ne ake kyautata zaton sun mutu a hatsarin na daren Juma’a zuwa Asubahin ranar Asabar.
Dandalin yanar gizo na kafar labarai ta Fox News ya ce hatsarin ya auku ne a hamadar Mojave da ke jihar California da daren jiya Jumma’a bisa ga bayanan hukumomi.
KU KUMA KARANTA:Tsadar abinci: Gwamnati za ta fara raba kayan abinci a faɗin Najeriya – Kwamiti
Dandalin na Fox News ya ce hukumomin Najeriya sun tabbatar da mutuwar Wigne a kafar sada zumunta, ciki har da Daraktar Hukumar Cinakayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala.
Kafar labaran ta Fox News ta ce cikin waɗanda suka mutu ɗin har da kuma tsohon Babban Chairman ɗin Nigerian Exchange Group, kuma wai fitaccen ɗan siyasa a Najeriya, Mista Godwin Obaseki, ya tabbatar da mutuwar matar Wigne ɗin da ɗansa.
Tuni dai kafafen yaɗa labaran Najeriya suka shiga yaɗa wannan labarin, ciki har da jaridar nan ta Premium Times.