Shugaban ƙasar Namibia Hage G. Geingob ya rasu ranar Lahadi a yayin da ake duba lafiyarsa a wani asibiti da ke Windhoek babban birnin ƙasar, a cewar wata sanarwa daga Fadar Shugaban Ƙasa.
Sanarwar wadda mataimakin shugaban ƙasar Nangolo Mbumba ya sanya wa hannu ta ce shugaban ya rasu ne a gaban mai ɗakinsa Madame Monica Geingo da ƴaƴansu.
“Ina mai baƙin cikin sanar da ku cewa shugaban ƙasarmu na Namibia abin ƙaunarmu Dr. Hage G. Geingob, ya mutu yau Lahadi, 4 ga watan Fabrairun 2024 da misalin ƙarfe 12 da minti huɗu a Asibitin Lady Pohamba inda likitocinsa suke kula da lafiyarsa,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta yi ƙira da ƴan ƙasar su kwantar da hankulansu, tana mai ƙarawa da cewa Majalisar Ministoci za ta yi taron gaggawa domin ɗaukar matakin da ya dace.
A watan jiya ne marigayin mai shekara 82 ya bayyana wa ƴan ƙasar cewa an gano yana fama da cutar daji.
Ofishinsa ya sanar cewa zai tafi Amurka domin yin jinya amma zai koma gida ranar 2 ga watan Fabrairu.
An zaɓi Mita Geingob a matsayin shugaban ƙasar Namibia a 2015 kuma yana yin wa’adinsa na biyu kuma na ƙarshe ne kafin rasuwarsa.
A watan jiya ne Shugaba Geingob ya caccaki matakin da Jamus ta ɗauka na goyon bayan “Isra’ila game da kisan ƙare-dangin da take yi wa fararen-hula da ba su da laifi a Gaza.”
KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya yiwa Gwamna Zulum ta’aziyya kan rasuwar mai magana da yawunsa
Ya ce sukar da Jamus ta yi wa Afirka ta Kudu saboda gurfanar da Isra’ila a gaban Kotun Ƙasa da Ƙasa a kan kisan ƙare-dangin da take yi a Gaza ya “girgiza” ƙasarsa.
Jamus ba ta da ƙimar da za ta kare “gwamnatin Isra’ila bisa kisan kare-dangi da take yi wa fararen-hula da ba su da laifi a Gaza da yankin Falasɗinu da aka mamaye,” in ji Namibia.
”A ƙasar Namibia, Jamus ta gudanar da kisan ƙare-dangi na farko a ƙarni na 20 daga shekarar 1904-1908, inda dubban ƴan ƙasar Namibia da ba su ji ba, ba su gani ba suka mutu cikin wulakanci,” kamar yadda Fadar shugaban ƙasar Namibia ta bayyana a wata sanarwa.