Shugaban ƙasa ya nuna damuwarsa kan rashin wuta a arewacin Najeriya

0
32
Shugaban ƙasa ya nuna damuwarsa kan rashin wuta a arewacin Najeriya

Shugaban ƙasa ya nuna damuwarsa kan rashin wuta a arewacin Najeriya

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana damuwarsa kan halin duhu da ake ciki a arewacin Najeriya sakamakon rashin wuta tsawon mako guda.

A sanarwar da mai ba shi shawara na musamman kan watsa labarai Nayo Onanuga ya fitar a ranar Litinin, ya ce a yanzu Shugaban Ƙasar ne jan ragamar koƙarin kawo ƙarshen rashin wutar wadda ta kawo tsaiko da durƙusar da harkokin tattalin azriki da zamantakwa.

Sanarwar ta kuma cewa Shugaba Tinubu ya nemi ganin Ministan Makamashi Adebayo Adelabu da Babban Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro Nuhu Ribadu kan batun.

“Shugaban Ƙasar ya umarci Ministan Makamashi da sauran hukumomin da suka dace da su gaggauta aikin dawo da wutar lantarki a dukkan yankinan da abin ya shafa a Arewa.

“Shugaba Tinubu ya yi bakin ciki da rahotannin ɓarna da lalata kayayyakin wutar lantarki da sauran ƙadarorin al’umma da suka yi sanadin jefa yankin a cikin duhu.

A ganawar da ya yi da Ministan Wutar Lantarki, Mista Adebayo Adelabu, wanda ya yi bayani kan kokarin da Kamfanin Samar da Lantarki na Najeriya ya yi na gyara layukan da suka lalace daga Shiroro zuwa Kaduna, sanarwar ta ce Shugaban Ƙasar ya ba da umarnin a magance matsalar a mataki na dogon zango.

KU KUMA KARANTA: Katsewar wutar lantarki a Najeriya, ta jefa alummar ƙasar cikin duhu

Shugaba Tinubu ya buƙaci injiniyoyin TCN da kada su yi ƙasa a gwiwa wajen kawo ɗauki cikin gaggawa ga mutanen da ke buƙatar wutar lantarki domin ci gaba da harkokinsu na zamantakewa da tattalin arziki.

Don ganin an ci gaba da aikin farfaɗo da aikin ba tare da tangarɗa ba, Shugaba Tinubu ya kuma umurci mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, da ya haɗa kai da sojoji da sojojin sama domin aikewa da isassun jami’an tsaro da suka hada da jirgin sama domin kare injiniyoyin da ke gyara layin da ya lalace.

Shugaba Tinubu ya roƙi sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma, da sauran shugabannin da su haɗa kai da hukumomin tsaro domin kare ƙadarorin jama’a da ababen more rayuwa.

Ya ce gwamnati ba za ta sake lamuntar da gangan a yi zagon ƙasa da lalata kayayyakin amfanin jama’a ba.

Matsalar ta fara ne tun daga ranar Litinin 21 ga watan Oktoba kana ya shafi yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma da kuma wasu sassan yankin Arewa ta tsakiya a Najeriya inda duk suka kasance cikin duhu.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabar sashen hulɗa da jama’a na Kamfanin TCN Ndidi Mbah ta ce kamfanin yana aiki ba dare, ba rana wajen ganin an dawo da hasken wutar lantarki a yankin duk da ƙalubalen tsaro da ma’aikatan kamfanin ke fuskanta.

Kamfanin ya ce dajin da matsalar ta faru waje ne da ma’aikatar ka yi fuskantar barazana daga ’yan fashin daji.

Ko da yake sanarwar ta ce kamfanin tare da taimakon ofis din Babban Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro, jami’an tsaro sun yi wa ma’aikatan kamfanin da ke aikin warware matsala rakiya don ganin cewa an dawo da hasken wutar lantarki ba tare da ba ta lokaci ba.

Sannan sanarwar ta ce jama’a su yi watsi da masu yada jita-jitar cewa gyara zai ɗauki lokaci mai tsawo sosai.

Tun bayan faruwar matsalar, mutane da yawa sun shiga cikin wani hali musamman wadanda ke asibiti neman lafiya da jarirai da ke buƙatar kulawa ta musamman da kuma wuraren ajiyar magungunan da ke buƙatar sanya a cikin firgi.

Haka ’yan kasuwa da masu sana’o’in hannu da iyalai da sauran harkokin yau da kullum a arewacin kasar sun shiga halin-ni-’ya-su kasancewa yadda galibin harkokin rayuwa suka dogara da wutar lantarki.

A baya idan aka samu ɗauke wutar lantarki na tsawon lokaci a ƙasar, wasu ’yan ƙasar musamman masu sana’o’i hannu kamar teloli da masu aski da sauransu sukan sayi man fetur ne don su ci gaba da sana’o’insu kafin a samu wutar lantarkin.

Sai dai a wannan lokaci hakan yana yi wa masu sana’o’i wahala kasancewa man fetur kansa shi ma farashin ya yi sama sosai, inda yanzu ake sayar da lita ɗaya a kan aƙalla naira 1,000.

Leave a Reply