Shugaba Tinubu zai wuce Landan daga Paris

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya kammala ziyarar aiki da ya kai birnin Paris na Faransa, inda kuma zai wuce birnin Landan a yau Asabar, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana.

Tun farko an tsara Tinubu zai koma gida Abuja ne bayan kammala taron, wanda shugabannin Afirka suka tattauna harkokin kasuwanci da zuba jari a nahiyar.

“Sai dai yanzu zai wuce birnin Landan na Birtaniya don yin wata ziyara ta ƙashin-kansa,” a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa shugaban zai koma gida kafin bikin Idin Babbar Sallah, wanda za a fara ranar Laraba.

A ranar Talata Tinubu ya tafi Paris bisa rakiyar wasu daga cikin masu ba shi shawara.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *