Shugaba Tinubu ya ce baya ga ministocinsa, mutane ƙalilan ne kaɗai ya amince su rinƙa shiga taron zaman majalisar zartarwa na ƙasa (FEC).
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ɗansa Seyi da wasu mutane da ke fadar shugaban ƙasar su daina shiga taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya wato FEC.
Shugaban ƙasar ya bayyana haka a lokacin taron majalisar a ranar Talata.
Tinubu ya ce ya lura ɗansa Seyi da wasu mutane da ba a amince su shiga taron ba suna shige-da-fice a ɗakin taron a makon jiya a yayin da ake tattaunawa kan muhimman abubuwa da suka shafi ƙasar.
Ya gargaɗe su game da wannan ɗabi’a tare da yi musu hani da aikata hakan.
Shugaban ya lissafo sunayen mutum huɗu waɗanda ya ce su kaɗai ya amince su halarci taron bayan ministocinsa.
A makon da jiya, na lura da wasu mutane suna shige-da-fice a yayin wannan taron, na ga hoton dana Seyi yana zaune a baya.
Ba za a yarda da wannan ba, zan sanar muku mutanen da suka kamata su kasance a nan,” in ji shi.
KU KUMA KARANTA: Iran ta gargaɗi Isra’ila kan ci gaba da kai hari kan Falasɗinawa
Shugaban ya ce waɗanda ya amince su halarci taron sun haɗa da mai ba shi shawara kan harkokin tsare-tsare Hadiza Bala Usman da mai taimaka masa kan bayanai da dabaru Bayo Onanuga da sakatarensa na musamman Hakeem Muri-Okunola da sakatarensa Damilotun Aderemi.
Ya ƙara da cewa waɗannan ne kaɗai ya amince su zauna a taron, sai dai idan shi ya buƙaci wani ya shigo taron.
Tinubu ya kuma gargaɗi Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnati da su kula da abin da ya faɗa kan wannan lamarin.









