Shugaba Tinubu ya naɗa jarumi Ali Nuhu da wasu mutane 10 muƙamai

0
128

Shugaba Najeriya Bola Tinubu ya amince da naɗin jarumi Ali Nuhu a matsayin Manajan Darakta na Hukumar tace Fina-Finai ta Najeriya da wasu mutane goma a matsayin shugabannin hukumomin da ke ƙarƙashin ma’aikatar fasaha, al’adu, da tattalin arziki.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Juma’a.

KU KUMA KARANTA: Shugaban Najeria, Tinubu, ya naɗa sabbin shugabannin hukumar Hajji ta ƙasa

A cewar sanarwar, “Shugaban ƙasa ya umurci waɗanda aka naɗa su gudanar da ayyukansu bisa ka’idojin ƙwarewa, ƙwazo, da kishin ƙasa da nufin ganin ɓangaren ya ƙara nutsuwa da kwarjini.

Leave a Reply