Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya dakatar da Ministar Ma’aikatar Jin-ƙai Betta Edu kan zargin badaƙalar miliyoyin kuɗaɗe.
An dakatar da Minista Edu ne kwana guda bayan shugaban ƙasar ya umarci a gudanar da bincike a kanta bisa zargin badakalar naira miliyan 585.
Shugaba Tinubu ya bai wa EFCC umarnin gudanar da bincike mai zurfi kan duk wasu hada-hadar kuɗi na Hukumar Kula da Ayyukan Jin-ƙai ta Najeriya
Haka kuma shugaban ƙasar ya bayar ga umarni ga babban sakataren hukumar ya karbi ragamar jagorancin hukumar, tare da buƙatar ministar kan ta bai wa hukumomi haɗin kai domin gudanar da bincike a kanta.
KU KUMA KARANTA: Shugaba Tinubu ya bada umarnin a binciki ministar jin-ƙai, Betta Edu
An yi ce-ce-ku-ce tun daga makon da ya gabata bayan wasu takardu sun nuna cewa Ministar Jinkai Betta Edu ta bayar da umarni ga Akanta Janar ta Najeriya ta tura naira miliyan 585 ga asusun wata mata mai suna Onlyelu Bridget Mojso a matsayin tallafi na shirin bayar da kuɗi ga marasa galihu.
Sai dai Akanta Janar ta Najeriya Dakta Oluwatoyin Madein ta ce ofishinta ba ya biyan kuɗi a madadin ma’aikatu da gwamnati kan ayyukan da suke aiwatarwa.
Bayan da ce-ce-ku-cen ya soma yawa sai Shugaba Tinubu ya bayar da umarni a soma bincike kan wannan lamarin inda daga baya aka dakatar da ita.