Shugaba Tinubu ya dakatar da kodinetan hukumar NSIPA, Halima Shehu

0
348

Tinubu ya dakatar da shugaba kuma ko’odineta ta hukumar kula da harkokin zuba jari ta ƙasa (NSIPA) Halima Shehu na wani ɗan lokaci daga muƙaminta.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan dakatarwar da aka yi a gidan talabijin na ƙasa a hukumance a wani shiri kai tsaye a ranar Talata, 2 ga watan Janairu.

Har yanzu ba a tantance takamaiman musabbabin dakatar da ita ba, duba da naɗin da aka yi mata watanni kaɗan da suka gabata.

Sai dai wata majiya na cewa shugaba Tinubu ya dakatar da shugabar ne bisa zargin zamba a hukumar.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Shari’a ta dakatar da Alkali kan yanke hukunci ta hanyar da ba ta dace ba

An ce mata ta sauka daga muƙaminta domin ba da damar gudanar da cikakken bincike kan zargin da ake mata.

A halin yanzu, shugaban ƙasar ya naɗa Mista Akindele Egbuwalo a matsayin kodinetan riko na NSIPA, har sai an kammala cikakken binciken da shugaba Tinubu ya bayar.

Ya zuwa yanzu, shi ne kodinetan shirin N-Power na ƙasa, kuma sabon naɗin nasa ya fara aiki nan take.

Tinubu ya naɗa Halima Shehu a watan Oktoba 2023, kuma Majalisar Dattawa ta tabbatar da naɗin nata a ranar 18 ga Oktoba, 2023.

Ta yi aiki a matsayin mai kula da shirin Cash transfer na ƙasa, inda ta yi amfani da ƙwarewar aikinta na banki da aikinta don ganin an daidaita shirin.

Leave a Reply