Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministoci

0
37
Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministoci

Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta tabbatar da sabbin ministoci

Majalisar Dattawa ta karɓi buƙatar neman tabbatar da naɗin sabbin ministoci 7 da ya tura sunayensu a jiya Laraba.

Buƙatar Shugaba Tinubu ta neman a gaggauta tabbatar da ministocin na ƙunshe ne a cikin wasiƙar ɗaya aikewa Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya Godswill Akpabio wanda ya karantata a farkon zaman majalisar na yau Alhamis.

Tinubu ya buƙaci majalisar ta yi nazari tare da tabbatar sunaye 7 da ya naɗa a matsayin ministoci.

Ministocin da ake neman a tabbatar din sun haɗa da Nentawe Yilwatda ta ma’aikatar jin kai da rage talauci, da Muhammad Maigari Dingyadi na ma’aikatar kwadago da ayyukan yi da, Bianca Odumegwu-Ojukwu karamar minista a ma’aikatar kasashen waje da kuma Jumoke Oduwole ta ma’aikatar masana’antu, ciniki da zuba jari.

Sauran sun haɗa da Idi Mukhtar Maiha na ma’aikatar bunƙasa kiwon dabbobi, da Yusuf Ata, karamin minista a ma’aikatar gidaje da raya birane sai kuma Suwaiba Ahmad, ƙaramar ministar ilimi.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya rushe maaikatar ci gaban yankin Neja-Delta da ta wasanni

Akpabio ya miƙa sunayen ga babban kwamitin majalisar domin kammala ayyukan majalisa akansu ba tare da ɓata lokaci ba.

Leave a Reply