Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan badaƙalar naira miliyan 585.189 da ake zargin ministar jin-kai, Beta Edu.
Wannan na zuwa ne bayan wasu ƙungiyoyi da sauran jama’a suka riƙa matsa wa Tinubu lamba kan a gudanar da bincike tare da ma hukunta ministar matuƙar aka same ta da laifi.
Ƙungiyoyin sun buƙaci Tinubu ya sauke Betta Edu daga muƙaminta don samun damar gudanar da ingantaccen bincike ba tare da samun wani katsalandan ba.
Tun da farko an zargi Betta Edu ne da rubuta wa Akanta-Janar ta Najeriya wata wasika da ke buƙatar ta sanya waɗannan kuɗaɗe a cikin asusun wata mata da ba a san kowace ce ba, lamarin da ya tayar da ƙura.
KU KUMA KARANTA: EFCC ta gayyaci tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Farouk
Sai dai jim kaɗan bayan fitar labarin, Akanta-Janar din ta ce ba ta saki waɗannan kuɗaɗen ba, saboda doka sam ba ta ba ta damar sanya kuɗaɗe a asusun wani mutum ba.
Ya zuwa yanzu dai ofishin ministar ya ce ta umarci a biya waɗannan kuɗaɗe ne don bai wa marasa galihu a Jihohin Akwa Ibom, Legas, Kuros Ribas da Ogun a matsayin tallafi.