Shugaba Tinubu ya amince da a sayarwa Ɗangote matatar man fetur

0
78
Shugaba Tinubu ya amince da a sayarwa Ɗangote matatar man fetur

Shugaba Tinubu ya amince da a sayarwa Ɗangote matatar man fetur

Daga Ibraheem El-Tafseer

Majalisar ministocin Tinubu ta amince da sayarwa Dangote matatar man fetur kan farashin Naira (ba dala ba) don samar da man fetur mai sauƙi a Najeriya.

Haka zalika Gwamnati Najeriya za ta dakatar da sayo man fetur daga ƙasashen waje don bunƙasa kamfanin Matatar Ɗangote tare da ba ta tallafin man fetur mai rahusa.

Shugaban ƙasa ya umarci NNPC ta amince da wannan tayin nasu don kawo sauƙi ga ‘yan Najeriya.

Shugaba Tinubu ya miƙa tayin tallafi ga matatar man Ɗangote ta hanyar ba da shawarar ga NNPC ta sayar da ɗanyen mai ga matatar Ɗangote a farashin Naira, ta yadda zai samar da rayuwa mai sauƙi ga ƴan Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Kalaman wasu jami’an gwamnatin Najeriya kan matatar man Ɗangote tamkar kwancewa ƙasar zani a kasuwa ne – Masana

Matatar Ɗangote a halin yanzu tana buƙatar jigilar ɗanyen mai guda 15 a duk shekara, wanda ya kai dala biliyan 13.5. Kamfanin NNPC ya yi alƙawarin samar da guda huɗu daga cikin waɗannan kayayyaki.

A nasa tsammanin matukar wannan kudiri ya tabbata za’a sayar da man fetur cikin farashi mai rahusa.

Leave a Reply