Shugaba Tinubu na zawarcin masu zuba jari daga ƙasar Faransa

0
13
Shugaba Tinubu na zawarcin masu zuba jari daga ƙasar Faransa

Shugaba Tinubu na zawarcin masu zuba jari daga ƙasar Faransa

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya shaidawa ‘yan kasuwar Faransa cewa kasarsa na maraba da harkokin kasuwanci, inda yace gwamnatinsa na samar da kyakkyawan yanayin da zai taimaka musu cin nasara.

Tinubu ya bayyana hakan ne a yau Alhamis yayin jawabin hadin gwiwa tsakaninsa da Shugaban Faransa Emmanuel Macron a fadarsa ta Elysee Palace.

“Yanzu muna inganta al’amura a bangaren tsaro. Ina mai bawa dukkanin masu niyar zuba jari tabbacin cewa Najeriya na maraba kuma a shirye take domin kasuwanci.”

“Muna baku tabbaci game da budaddiyar kasuwa; komai cikin sauki, ba tare da matsala ba,” a cewar Tinubu.

KU KUMA KARANTA:Najeriya za ta samar da wutar lantarki mai ƙarfin megawatt dubu 14 – Ministan Lantarki

Shugaban na Najeriya ya kuma yi tsokaci game da matasan kasar dake da dimbin basira da ilimi sannan yace a shirye suke su karbi horo a matsayin wani bangaren na dalilan da za su sanya ‘yan kasuwar Faransa karkata ga kasar dake yammacin Afirka.

Ya kara da cewa Najeriya na kokarin fadada tattalin arzikinta ya zarta harkar danyen mai kuma ya yi amanar cewa Faransa za ta taka muhimmiyar rawa kan hakan.

Shugaba Tinubu ya yabawa gwamnatin Faransa a kan samar da daidaito domin gudanar kasuwancin Najeriya a kasar ta nahiyar Turai.

Leave a Reply