Shugaba Ruto na Kenya ‘ba zai’ sa hannu a kan sabuwar dokar ƙarin haraji ba
Shugaban Kenya, William Ruto ya ce ba zai rattaba hannu kan wata doka mai cike da cece-kuce da ta haifar da zanga-zanga a faɗin ƙasar ba, har aka harbe mutane da dama.
Masu zanga-zangar sun mamaye majalisar ne bayan da ‘yan majalisar suka zartar da dokar a ranar Talata. Kudirin zai kara yawan haraji da kuma tsadar rayuwa.
“Bayan yin la’akari da ci gaba da tattaunawa game da abubuwan da ke ƙunshe a cikin kudirin kudi na 2024, da kuma sauraron jama’ar Kenya, wadanda suka yi kira da babbar murya cewa ba sa son wani abu da wannan ƙudirin kuɗi na 2024, na yarda, don haka ba zan sanya hannu ka dokar ba, kuma daga baya za a janye shi,” Ruto ya shaida wa taron manema labarai a fadar gwamnati da ke Nairobi babban birnin ƙasar.
KU KUMA KARANTA: Adadin waɗanda suka mutu a tarzomar Kenya ya ƙaru
“Mutane sun rasa rayukansu kuma abin takaici ne matuka, da ma hakan bai faru ba,” ya ƙara da cewa.
Zanga-zangar ta jawo gwamnati ta girke sojoji don shawo kan karya doka da oda.
Sai dai wata Babbar Kotu ta soke umarnin girke sojojin.