Shugaba Erdogan ya sha alwashin taimaka wa waɗanda girgizar ƙasa ta shafa a watan Fabrairun 2023 a Turkiyya

0
142

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi alƙawarin faranta rayukan waɗanda girgizar ƙasar bara ta shafa. 

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi alƙawarin faranta rayukan waɗanda girgizar ƙasar da ta afku a yankin kudancin ƙasar a ranar 6 ga watan Fabrairun 2023 ta shafa.

“Zafin rayukan da muka rasa a girgizar ƙasar da ta faru wacce ta fi muni a Kahramanmaras, wacce muka fuskanta shekara guda da ta wuce, na ci gaba da ƙona zukatanmu tamkar yau abin ya faru,” in ji Erdogan a yayin tunawa da ranar farko ta girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske da ta kashe mutum 53,537 tare da jikkata wasu fiye da 107,000.

Ɓarnar da aka samu a larduna 11, waɗanda ke cikin tsofaffin matsugunai a tarihin ɗan’adam, “ta yi girma ƙwarai da gaske,” in ji Shugaban.

Girgizar ƙasa masu ƙarfin maki 7.7 da 7.6 sun afku ne a larduna 11 na Turkiyya – Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Elazig da Hatay da Gaziantep da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da Sanliurfa.

KU KUMA KARANTA: Girgizar ƙasa mai karfin gaske ta kashe mutane 296 a Maroko

Fiye da mutum miliyan 13.5 ne girgizar kasar ta shafa a Turkiyya, da kuma wasu da dama a arewacin Siriya.

Edogan ya ƙara da cewa, irin waɗannan manyan bala’o’i da wahalhalun da ake fuskanta, matsaloli ne da suke koyar da jajircewa a inda ake gwada ƙarfin haɗin kai da ‘yan’uwantaka, inda ya ƙara da cewa, al’ummar ƙasar sun yi nasara a kan wannan jarrabawa mai raɗaɗi a tarihi.

Yayin da gwamnatin ƙasar ta ɗauki matakin gaggawa da dukkan ƙarfinta, Erdogan ya ce, Turkiyya ta haɗa kai wajen yaƙi da bala’in ƙarni.

Shugaban ya kuma jaddada cewa gwamnati na aiki tuƙuru domin ganin ta cika alkawuran da ta yi wa al’ummar ƙasar, shugaban ya ƙara da cewa, “Za mu ci gaba da wannan ƙoƙari har sai mun gina da kuma farfaɗo da garuruwanmu.

Leave a Reply