Shirin gwamnatin Kano na gina sabuwar gada a Ɗan-Agundi ya tayar da ƙura

0
210

Matakin da gwamnatin jihar Kano ta ɗauka na yin amfani da kuɗaɗen ƙananan hukumomi wurin gina wata gada a cikin birnin Kano ya jawo wa Gwamna Abba Kabir Yusuf suka.

Gwamnatin ta jihar Kano, a wata takarda da ofishin Babban Akanta na Jihar ya fitar, ta amince a kashe kusan naira biliyan goma sha shida domin gina gadar kasa da ta sama a unguwar Ɗan-Agundi da ke cikin birnin Kano.

Za a yi haɗin gwiwa tsakanin gwamnatin jiha da gwamnatocin ƙananan hukumomi wurin gina gadar inda jiha za ta bayar da kashi 30 yayin da kananan hukumomi za su bayar da kashi 70, in ji takardar.

“Don haka Majalisar Zartarwa ta jiha ta amince a fitar da naira biliyan shida da miliyan ɗari uku da tamanin da tara” a matsayin kuɗin kafin-alkalami ga ɗan kwangilar da zai yi wannan aiki, in ji gwamnatin.

Sai dai tuni wannan mataki ya soma fuskantar suka daga waɗanda suke gani bai kamata a yi amfani da kuɗin ƙananan hukumomi wurin gudanar da irin wannan aiki a cikin birni ba bayan kuwa su ne suka fi cancanta wurin samun ayyukan ci-gaba.

A gefe guda, wasu suna ganin gina gada a wannan lokaci da talakawa ke buƙatar ayyukan wajibi kamar samar da ruwan sha da gina asibitoci da makarantu da sauransu, ba shi ne ya zama abu mafi muhimmanci ba.

KU KUMA KARANTA: Sanata Barau ya ɗauki matakin dakatar da Shoprite daga ficewa daga Kano

Fitaccen lauyan nan na jihar Kano, Abba Hikima, ya yi tsokaci a kan hakan inda ya ce “Don Allah a tsayar da wannan aikin. Irin wadannan abubuwan ne suke sa wa mutane suke ɗauka gaba daya ashe ‘yan siyasa irinsu daya.

Yanzu saboda Allah ina adalci a nan? Kauyukan Kano suna cikin mawuyacin hali… amma a ɗauko kuɗinsu a saka a gada guda ɗaya?”

A baya dai, jami’an gwamnati mai ci sun rika sukar gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje kan gina gadoji, shi ya sa ma a wannan karon wasu suke sukarsu bisa shirin gina gadar ta Dan-Agundi.

Malam Abdul Aziz Abdul Aziz, mai taimaka wa shugaban Najeriya kan watsa labarai, ya ce “Lokacin da na ga sanarwar gina waɗannan gadoji na yi wa wasu abokaina guda biyu personal message (saboda gudun magana a bainar jama’a ƴan baka su maida abin siyasa).

“Abin da na rubuta musu shi ne idan har mun ta sukar Ganduje a kan kashe maƙudan kuɗaɗe don gina gadoji alhali akwai bukatu na gaggawa ban ga dalilin yin shiru a kan gadar Tal’udu da sauran da Abba yake shirin yi ba.”

Ita ma Nanerh Hawwerh cewa ta yi “Maganar gaskiya, ni kaina ba na goyon bayan wannan aikin, akwai ƙauyuka da suke da buƙata fiye da wannan aikin. Don Allah mahunkunta su duba wannan al’amari.”

Sai dai a nasa ɓangaren, Aliyu Dahiru Aliyu, ya ce: “Harkar ci-gaban jiha haduwa ake a yi tare. Kuɗin revenue da ake samu a jihar nan fiye da rabinsa a local governments ba su fi biyar zuwa shida na birni ake tattara su ba. Amma a haka ake diba a yi wa na Doguwa da na Tsanyawa aiki.”

Kawo yanzu gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba ta yi raddi kan wannan batu ba, sai dai wasu na ganin za ta iya sauya matsayinta idan aka yi la’akari da shawarwarin da aka ba ta a baya kan wasu matakai da ta ɗauka, waɗanda ba su yi wa mutane dadi ba.

Leave a Reply