Shettima ya wakilci shugaba Tinubu wajen jana’izar Sarkin Zuru
A ranar Juma’a Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen jana’izar Sarkin Zuru, Manjo-Janar Muhammadu Sani Sami (ritaya), wanda aka yi a garin Zuru, Jihar Kebbi.
A wajen jana’izar, Shettima ya jaddada gagarumar gudummawar da marigayi Sarkin ya bayar, waɗanda ya ce ba za a taɓa mantawa da su ba.
KU KUMA KARANTA: Sarkin Zuru Muhammad Sami ya rasu a Landan
Ya ce, “Ana girmama sarakunan gargajiya a ƙasar mu saboda rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya.”

Shettima ya jagoranci tawagar Gwamnatin Tarayya zuwa wajen jana’izar kuma ya isar da gaisuwar Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ga gwamnatin Jihar Kebbi da iyalan marigayin da kuma dukkan al’ummar jihar.

Ɗimbim sarakuna, jami’an gwamnati, ‘yan kasuwa da sauran mutane sun halarci taron jana’izar.









