Shekara 1 Akan Mulki: Gwamnatin Kaduna ta yiwa al’umma aiki kyauta

Shekara 1 Akan Mulki: Gwamnatin Kaduna ta yiwa al’umma aiki kyauta

Daga Idris Umar, Zariya

An ƙaddamar da aiki kiwon lafiya ƙyauta don cikar gwamnatin sanata Uba Sani shekara ɗaya a babban asibitin garin maƙarfi a jihar Kaduna.

Wakilanmu ya ziyarci wannan asibitin don ganewa idonsa yadda aikin ke gudana.

Manyan likitocine da ƙanana suke gudanar da aiyukan a ɓangarori rashin lafiya daban daban.

Neptune Hausa ya zanta da wata mata wacce akayi mata aiki a idanunta mai suna Salamatu daga garin Auchan.

KU KUMA KARANTA: Sabbin matakan bai wa makarantun jihar Kaduna tsaro
Malama Salamatu tace, anyi mata aiki kyauta ƙarkashin gudummawar gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani bisa haka tayi wa Gwamna addu’ar Allah ya taimakeshi kamar yadda ya taimaka masu.

Malam Adamu Abubakar daga shiyar Kudan wanda aka yiwa yaransa guda biyu aikin cire ƙaba shima addu’a yayiwa gwamna tare da nuna jin daɗinsa da wannan ƙokari.

Dakta Ahmad Aliyu shine shugaban ayarin likitocin da suke gudanar da wannan aiki.

Dakta Ahmad yace,sunzo babban asibitin ne don ƙaddamar da akin lafiya kyauta karkashin Primary Health care  wato shirin kiwon lafiya a matakin farko wanda mai girma Alhaji Bello Jamo ke jagoranta a faɗin gwamnatin jihar Kaduna ta Sanata Uba Sani, bisa alƙawarin da yayi na baiwa harkar lafiya muhimmanci a gwamnatin sa baki ɗaya.

Likitan ya ƙara da cewa ayarin likitocine wasu daga asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika Zariya suke wato haɗin guiwa kenan.

Tuni suka fara gudanar da aiki a ɓangarori daban daban kamar aikin cire ƙaba da akin Idanu da duba masu Hawan jini da masu taifot da maleriya da ciwon suga.

Likitan yace zasu duba mutane ɗaruruwa har tsawon kwanaki huɗu.

Kuma akin duk sunayi shi ƙarƙashin kulawar sakataren harkar lafiya na gwamnatin jihar Kaduna ne kuma suna samun goyon baya a wajan sa a matsayinsa na shugaba haka suma mutane suna bada haɗin kai sosai komi na tafiya yadda ya kamata.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *