No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sanannen Malamin Addinin Musuluncin nan kuma Shugaban masu Ilimin Taurari na Afirka, Sheikh Muhajjadina Sani Kano ya yi tir da kisan da aka yi wa masu gudanar da bikin mauludi fiye da 77 da jirgin saman sojojin Nijeriya ya yi a ƙauyen Tudun Biri da ke ƙaramar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna ranar Lahadin da ta gabata.

Sheikh Muhajjidina ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a Kano, ya kuma ce, wannan kisan na gangaci ne kuma abin da ya kamata al’ummar Nijeriya su yi tir da shi ne kuma a tabbatar da an biya diyyar dukkan waɗanda aka kashe.

Ya ƙara da cewa, wannan ba shi ne na farko ba da jami’an tsaro ke hallaka fararen hula a bisa kuskure ba, a saboda haka ya zama dole shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gudanar da cikakken bincike tare da tabbatar da an hukunta dukkan masu hannu a kan wannan ta’asar a kuma tabbatar da an biya diyyar dukkan waɗanda aka kashe ga iyalansu, “Don haka ya zama darasi a nan gaba.

Ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓi shahadar waɗanda suka rasu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...