Shaye-shaye ke rura matsalar tsaro a Yobe — Sarkin Fika

0
148

Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar Yobe, Dokta Muhammadu Abali Ibn Muhammadu Idrissa, ya bayyana shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a matsayin abin da ke rura wutar rashin tsaro a jihar. 

Sarkin ya bayyana haka ne a lokacin wata liyafa da ya shirya ga ’yan jarida a fadarsa da ke ƙaramar hukumar Potiskum.

Ya ce harin baya-bayan nan da aka kai a yankin Gurjaje da ke ƙaramar hukumar Fika ta jihar, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum daya tare da lalata gidaje sama da 100, ya tabbatar masa da alakar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da rashin tsaro.

KU KUMA KARANTA: An ba da umarnin ƙara tsaro a rumbunan NEMA don gudun masu warwason kayan abinci

Sarkin Fika ya buƙaci gwamnatin jihar da Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta fito da tsare-tsaren da za su dakile ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar.

Ya kuma yi ƙira ga gwamnati da ta samar da cigaba a yankunan da lamarin ya shafa, yana mai kokawa kan taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasar.

Leave a Reply