Shaye-shaye barazana ce ga goben Najeriya, Buba Marwa ya gargaɗi matasa

0
160
Shaye-shaye barazana ce ga goben Najeriya, Buba Marwa ya gargaɗi matasa
Shugaban NDLEA, Buba Marwa

Shaye-shaye barazana ce ga goben Najeriya, Buba Marwa ya gargaɗi matasa

Daga Jameel Lawan Yakasai

Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Manjo Janar Buba Marwa (mai ritaya), ya bayyana cewa shan miyagun ƙwayoyi a tsakanin matasa na daga cikin manyan abubuwan da ke yi wa makomar Najeriya barazana.

Marwa ya yi wannan gargadi ne a Abuja yayin wani shirin kwallon ƙafa na wayar da kan matasa kan illolin miyagun ƙwayoyi mai taken “Kick Out Drug Abuse” (KODA), wanda Richy Gold International Ltd ta shirya tare da haɗin gwiwar NDLEA.

Ya ce matasa na ta amfani da ƙwayoyi irin su taba, giya, wiwi, tramadol, codeine da hodar iblis a makarantu da yankunan al’umma, abin da ke illa ga lafiyarsu da makomarsu.

“Waɗannan ƙwayoyi na jawo rugujewar iyalai, ɓata tunani, tashin hankali da ƙaruwar aikata laifuka,” in ji shi.

KU KUMA KARANTA: NDLEA a Kano ta kama tabar wiwi da kwalaben Akurkura dubu 8

Shugaban NDLEA ya jaddada cewa rigakafi shi ne mafi ingancin kariya, inda ya yaba da amfani da kwallon ƙafa wajen jawo matasa zuwa hanyar kirki da nisantar da su daga miyagun ɗabi’u.

Ya kuma yi kira ga matasa da su rungumi taken “Kick Out Drug Abuse” a matsayin hanyar rayuwa, yana mai jaddada cewa babu ɗan kwallon da zai iya dorewa a wasa da rayuwa idan yana shan miyagun ƙwayoyi.

Shi ma Babban Daraktan Richy Gold International Ltd, Jude Onwusonye, ya bayyana cewa shirin KODA ba aiki ba ne kawai, illa dai kira ne na kare makomar matasa da kuma gina al’umma mai koshin lafiya da ci gaba.

Leave a Reply