Sha’aban Sharaɗa ya baiwa mazaɓarsa tallafin miliyan 57

0
360

Memba mai barin gado mai wakiltar mazaɓar Kano Municipal, Alhaji Sha’aban Sharaɗa, ya bayar da tallafin karatu na Naira miliyan 57 ga mazaɓarsa.

Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a ranar Lahadi a Kano, ɗan majalisar ya ce an baiwa ɗalibai kimanin 32 tallafin karatu na sama da naira miliyan 7 don ci gaba da karatunsu a ‘National Open Univerfity’ Jami’ar Bayero Kano da ke Kano, yayin da aka raba naira miliyan 50 ga Jami’ar Alqalam, wanda hakan ya amfana ɗalibai daga mazaɓar sa.

Sharaɗa, wanda aka naɗa kwanan nan a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Almajirai da Marasa Makarantu ta Najeriya, ya ce matakin zai taimaka matuƙa wajen rage wa iyayensu nauyi.

KU KUMA KARANTA: Masallacin ƙasa na Abuja ya bayar da tallafin abinci ga ‘yan gudun hijira 400

Ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa harkokin ilimi, inda ya bayyana cewa za a ci gaba da bayar da tallafin karatu da tallafi tare da haɗin gwiwar magajinsa, Sagir Ƙoƙi.

Daga nan ya nuna jin daɗinsa da samun damar zama babban sakataren Hukumar Almajirai da Marasa Makaranta.

Ɗan majalisar ya jaddada sadaukarwar sa ga aikin hukumar tare da tabbatar wa da mahalarta taron cewa naɗin nasa zai yi tasiri sosai.

Sheikh Gwani Danzarga, wanda ya yi magana a madadin al’umma, ya bayyana jin daɗinsa a madadin al’umma saboda samun Sharaɗa a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Yaran Almajirai da Marasa Makaranta.

Ya jaddada cewa naɗin Sharaɗa ya dace sosai kuma ya nuna ƙwarin gwiwa kan yadda zai iya yin tasiri mai kyau a kan manufofin hukumar.

Taron ya samu halartar wakilai daga ƙanana da matsakaitan masana’antu na Najeriya, SMEDAN, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka masu alaƙa, ICPC da kuma hukumar kula da iyakoki ta ƙasa.

Leave a Reply