SEMA ta ceto wani matashi a Yobe da ya yi yunƙurin kashe kansa, saboda ƙuncin rayuwa

0
348

Daga Ibraheem El-Tafseer

Hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Yobe (YOSEMA) ta ceto wani matashi ɗan shekaru 30 da haihuwa (an sakaya sunansa) a Damaturu, babban birnin jihar daga yunƙurin kashe kansa saboda halin da ake ciki ƙuncin rayuwa.

A cewar shaidun gani da ido, wanda ya tsiran mazaunin gidajen Mai Mala, daura da Titin Gashuwa-Damaturu a Jihar Yobe wanda saboda takaici da matsin tattalin arziƙi da ya fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi, ya yi yunƙurin kashe kansa ta hanyar shan gubar Ɓera.

Da lamarin ya faru, sai mutanen hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar (SEMA) suka bazama wurin da lamarin ya faru, inda suka garzaya da mutumin asibiti inda likitoci suka yi masa maganin kashe ƙwayoyin cuta, suka yi masa magani tare da yi wa wanda abin ya shafa nasiha.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun cafke mutumin da ya yi yunƙurin cinnawa masallaci wuta

An ruwaito cewa saƙon ya isa ga SEMA ta hannun ’yan banga na yankin da mahaifiyar matashin ta sanar da su. SEMA ta tabbatar da cewa wanda ya tsira yana karɓar magani.

Duk da haka, gwamnatin jihar ta hannun SEMA ta taimaka wa dangi da kayan abinci don rage illa da wahalhalu.

Da yake tabbatar da rahoton, babban sakataren ƙungiyar ta YOSEMA, Dakta Mohammed Goje ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici.

“Eh gaskiya ne, amma nan da nan aka tura mazana zuwa wurin bayan da muka samu ƙiran gaggawa daga wasu nagartattun samari.

“A halin yanzu matashin yana karɓar magani.” Goje ya bayyana. Menene ra’ayinku game da waɗannan al’amura marasa kyau da cire tallafin man fetur ya haifar? ya tambaya.

Leave a Reply