Sauyin Takardun Kuɗi: Shugaba Buhari zai yi wa ‘yan ƙasa jawabi

1
533

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari zai yiwa al’umar ƙasa jawabi a ranar Alhamis 16 ga watan Fabrairun 2023 da ƙarfe 7 na safe.

A wata sanarwar da mai baiwa shugaban ƙasa shawara na musamman kan al’amurran da suka shafi yaɗa labarai, Femi Adesina ya sanya wa hannu ya ce an umarci gidajen alabijin da gidajen rediyo da sauran kafafen yaɗa labarai na zamani da su kawo jawabin kai tsaye da daga gidan Talabijin na ƙasa wato NTA da Rediyon Najeriya domin yada shirye-shiryen jawabi da shugaba Buhari zai gabatar.

1 COMMENT

Leave a Reply