Saudiyya ta hana Sheikh Gumi shiga ƙasar domin aikin Hajji

0
296
Saudiyya ta hana Sheikh Gumi shiga ƙasar domin aikin Hajji

Saudiyya ta hana Sheikh Gumi shiga ƙasar domin aikin Hajji

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumomin Saudiyya sun hana Sheikh Ahmad Gumi shiga ƙasar domin gudanar da aikin Hajjin bana, duk da cewa sun ba shi biza ta izinin shigowa ƙasar.

A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Gumi ya ce: “Bisa wasu dalilai da suka shafi ra’ayina game da siyasar duniya, hukumomin Saudiyya ba sa son in kasance a aikin Hajji duk da sun ba ni biza.”

Ya ce hukumomin Najeriya sun sha alwashin tuntuɓar ƙasar Saudiyya domin jin dalilin hana shi shiga ƙasar.

Bayanan da BBC HAUSA ta tattara sun nuna cewa Sheikh Gumi na cikin jerin malamai da Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta ɗauki nauyinsu domin gudanar da ibada a ƙasa mai tsarki.

KU KUMA KARANTA:Hukumar jindaɗin Alhazai a Kano ta fara raba kayan aikin Hajjin bana

Sheikh Gumi ya isa filin jirgin saman Madina ne da misalin ƙarfe 10:30 na dare a ranar Asabar da ta gabata, tare da sauran malamai cikin jirgin kamfanin Umza Air.

Sai dai bayan isarsu, jami’an shige da ficen Saudiyya sun hana Sheikh Gumi shiga cikin ƙasar, lamarin da ya sa dole ya koma Najeriya.

A halin yanzu, Sheikh Gumi ya dawo gida inda ya cigaba da karantarwa da sauran ayyukansa na yau da kullum.

Leave a Reply