Satifiket ɗin jami’ar Chicago, UGRFP ta buƙaci Tinubu ya fito fili ya wanke kansa

0
239

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata ƙungiyar farar hula, mai suna ‘United Global Resolve for Peace’, (UGRFP), ta yi ƙira ga Shugaba Bola Tinubu da ya fito ya wanke kansa kan rikicin satifiket ɗinsa na jami’ar Chicago, wanda ake cewa na bogi ne.

Ƙungiyar ta shawarci Tinubu da ya fito ya kare gaskiyarsa, ko dan ma ya kunyata magautansa.

Shalom Olaseni, shugaban UGRFP, ne ya faɗi hakan a yau Lahadi a cikin wata sanarwa cewa a matsayinsu na ƙungiya mai ruwa da tsaki, sun sanya ido kan duk dambarwar da ake yi kan sahihancin takardar shaidar kammala jami’ar ta Tinubu.

Olaseni ya ce lamarin ya ja hankalin kafafen yaɗa labarai na gida da waje.

“Yanzu ne lokacin da ya dace da shugaban ƙasa ya ba da duk wata shaida da ke nuna cewa an samu takardar shaidarsa da gaske,” in ji shi.

Mista Olaseni ya ce dimokuraɗiyyar Najeriya za ta shiga cikin halin rashin tabbas idan ba a warware taƙaddamar ba.

KU KUMA KARANTA: Kotu a Amurka ta umarci jami’ar Chicago ta bai wa Atiku damar ganin takardun karatun Tinubu

“A dangane da haka, muna ƙira ga shugaba Tinubu da ya fito fili ya bayyana ɓangaren sa na lamarin.

“Shugaban ƙasa, a matsayinsa na mai kula da shugabancinmu na ƙasa, al’ummar Nijeriya na da haƙƙin a kan sa da ya bayar da hujjojin da ba za a iya musantawa ba da ke tabbatar da sahihancin satifiket ɗin karatunsa,” in ji shi.

Leave a Reply