Sarkin Zazzau ya naɗa ɗansa a matsayin Walin Zazzau

0
595

Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, CFR, ya amince da naɗin ɗansa na fari, Abdullahi Ahmed Bamalli a matsayin sabon Walin Zazzau.

Hakan ya biyo bayan rasuwar tsohon Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Injiniya Aminu Umar, wanda ya rasu bayan gajeriyar jinya a ranar Lahadi.

Daily Trust ta gano cewa sarautar Wali a Masarautar Zazzau ita ce ta uku a cikin manyan Hakimai da sarakunan masarautar ke riƙe da su bayan sarautar Madaki da Magajin Gari.

A wata sanarwa da Abdullahi Aliyu Ƙwarbai, jami’in yaɗa labarai da bayanai na masarautar ya fitar, ta ce kakan Abdullahi Bamalli, Marigayi Walin Zazzau, Halliru ne ya fara riƙe sarautar.

KU KUMA KARANTA:Masarautar Zazzau ta dakatar da basarake kan yi wa matashi hukunci

Sanarwar ta kuma ƙara da cewa Sarkin ya kuma amince da naɗin Injiniya Sani Galadima Umar, ƙanin marigayi Walin Zazzau, Injiniya Aminu Umar a matsayin sabon Yariman Zazzau.

A tuna cewa tsohon Yariman Zazzau, Alhaji Munir Jafaru, shi ne tsohon Yariman Zazzau wanda tun daga lokacin ne sarki ya ɗaga likkafar sa zuwa matsayin ‘Madaki Zazzau’.

Leave a Reply