No menu items!

Sample Page Title

Date:

Sarkin yaƙin Zazzau Rilwanu Pate ya rasu

Daga Idris Umar, Zariya

Majalisar masarautar Zazzau ta sanar da rasuwan Sarkin Yakin Zazzau Alhaji Rilwanu Yahaya Pate.

Marigayi Allah Rilwanu Yahaya wanda yake Dan Majalisa ne a Masarautan Zazzau, ya kasance kuma a matsayin Kansila Mai lira da Fannin Kiwon Lafiya a Masarautan.

KU KUMA KARANTA:Allah Ya yi wa surkar Sarkin Zazzau rasuwa

Rasuwan nasa ya auku ne a Asibitin Gambo Sawaba wanda ke Kofan Gayan a inda suke halartan Taron Kwamitin Abokai na Asibitin tare da Mai Martaba Sarkin Zazzau da safiyan yau.

Za a sanar da lokacin da za gabatar da Jana’izar Marigayi Sarkin Yakin Zazzau Alhaji Rilwanu Yahaya Pate.

Da fatan Allah Ya jikanshi da rahama.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...