Sarkin Saudiyya ya yi ƙira kan kawo ƙarshen munanan laifukan da ake yi a Gaza

Sarki Salman na Saudiyya ya yi ƙira a cikin saƙonsa na watan Ramadan ga ƙasashen duniya da su kawo ƙarshen munanan laifukan da ke faruwa a Gaza, inda Isra’ila ta shafe sama da watanni biyar tana gwabza yaƙi a yankin.

Da yake magana a matsayin mai kula da wurare biyu mafi tsarki na Musulunci, Sarki Salman ya yi godiya kan “yadda aka albarkaci Masarautar Saudiyya”, amma ya ce yaƙin da ake yi a Gaza da aka yi wa ƙawanya zai sa a yi azumi da sauran ibadu cikin rashin walwala.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kashe gomman Falasɗinawa a ranar farko ta Azumin Ramadana

“Yayin da muke maraba da shigowar watan Ramadan a wannan shekara,ranmu ya yi matuƙar ɓacin kan yadda ‘yan’uwanmu Falasɗinawa ke ci gaba da fuskantar hare-haren wuce-gona-da-iri,” in ji shi.

“Muna ƙira ga ƙasashen duniya da su kiyaye nauyin da ke wuyansu na kawo ƙarshen waɗannan munanan laifuka tare da tabbatar da kafa hanyoyin jinƙai da na agaji.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *