Sarkin Maroko ya yi wa fursunoni sama da dubu 2 afuwa

0
45
Sarkin Maroko ya yi wa fursunoni sama da dubu 2 afuwa

Sarkin Maroko ya yi wa fursunoni sama da dubu 2 afuwa

An yi afuwa ko rage wa’adin zaman gidan kaso ga dubban fursunoni a Maroko, a wani ɓangare na bukukuwan murnar cikar Sarki Mohammed na IV shekaru 25 a kan mulki.

An yi afuwa ga fursunoni 1,476 da suka haɗa da ‘yan jarida uku, Omar Radi, Soulaimane Raissouni, da Taoufik Bouachrine, da mai fafutukar kare tarihi Maati Monjib.

Daga cikin waɗanda aka yi wa afuwa, 2,278 na tsare a kurkuku, yayin da 182 suke wajen kurkukun, in ji Ma’aikatar Shari’a.

Ba a tabbatar da ko ‘yan jaridar sun samu afuwar fita daga kurkuku ne ko rage yawan kwanakinsu ba.

KU KUMA KARANTA: Mahukuntan DR Congo sun yiwa fursunoni 1,200 afuwa da zummar rage cunkoso

Tun shekarar 2000 ake tsare da ‘yan jarida Omar Radi da Soulaimane Raissouni bisa zargin cin zarafin wata mace.

Ƙungiyar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Human Rights Watch ta zargi Maroko da amfani da kotuna “wajen danniya da zalunci” da manufar toshe bakunan ‘yan jarida da masu sukar gwamnati.

Kotun Ƙolin ƙasar ta yi watsi da ɗaukaka ƙara na ƙarshe da ‘yan jaridar suka yi a watan Yulin 2023.

Sarkin ya yi afuwa ga fursunonin da aka ɗaure bayan tuhumar su da laifukan tsaurin ra’ayi da ta’addanci.

Ma’aikatar Shari’a ta ce fursunonin sun samu amincewar masarauta bayan sake duba aƙidunsu da watsi da da tsaurin ra’ayi da ta’addanci da suka yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here