Sarkin Kuwait Sheikh Nawaf Al-Ahmad Al-Sabah ya rasu a ranar Asabar da safe.
Ministan Harkokin Masarautar Kuwait Mohammad Abdullah Al-Mubarak Al-Sabah ya ce sarkin ya rasu yana da shekara 86 da haihuwa.
A cewarsa, an kai sarkin asibiti da safe sakamakon buƙatar gaggawa amma daga baya Allah ya yi masa rasuwa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Kuwait ya ruwaito.
Ya bayyana cewa ko a watan da ya gabata sai da aka kai sarkin asibiti sakamakon rashin lafiyar da yake fama da ita.
KU KUMA KARANTA: Gwamnan Anambra na farko, Chukwuemeka Ezeife, ya rasu
Sheikh Nawaf ya zama yarima mai jiran gado a 2006, bayan ɗan uwansa Sheikh Sabah Al-Ahmad Al-Sabah ya naɗa shi.
Ya zama Sarkin Kuwait bayan rasuwar ɗan uwan nasa a Satumbar 2020 a lokacin da yake da shekara 91 da haihuwa.
A halin yanzu Sheikh Mishal Al-Ahmad Al-Sabah mai shekara 83 shi ne yarima mai jiran gado na ƙasar