Sarkin Kano ya aika wa Tinubu saƙo kan wahalar da jama’a ke ciki

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ya buƙaci matar shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta isar da saƙo ga mijinta kan cewa mutane na cikin yunwa da wahala a Najeriya.

Ya bayyana haka ne a fadarsa da ke Kano a lokacin da ta kai masa ziyara a ranar Litinin.

Mai ɗakin shugaban ƙasar ta ziyarci Kano ne domin bikin buɗe wani gini a tsangayar koyar da aikin lauya a Jami’ar Maryam Abacha inda aka saka wa ginin sunan matar shugaban ƙasar.

Sarkin na Kano ya shaida wa Oluremi cewa akwai hanyoyi da dama da za su iya aika saƙo ga shugaban ƙasa amma aika saƙo ta hanyar matarsa zai fi inganci.

“Muna samun saƙo daga al’ummar da muke shugabanta kusan kullum cewa abubuwa sun yi tsauri, abinci ya yi tsada, mutane suna cikin wahala,” in ji sarkin.

KU KUMA KARANTA: Ban ce na fi ƴan Najeriya shan wahalar tsadar rayuwa ba — Ɗangote

Ya bayyana cewa duk da ba a yanzu wannan lamarin ya fara ba, amma akwai buƙatar shugaban ƙasar ya ƙara ƙoƙari domin taimaka wa al’umma.

Baya ga saƙon halin talauci da sarkin ya ce jama’a na kokawa a kai, ya buƙaci matar shugaban ƙasar da ta ƙara jaddada masa kan halin da ake ciki dangane da tsaro a ƙasar inda ya ƙara jaddada cewa duk da ba a wannan lokaci wannan matsala ta fara ba, amma suna ci gaba da yi musu addu’a kan Allah Ya ba su ikon shawo kan matsalar.

Haka kuma sarkin ya ƙara bayyana mata wani ƙorafi da jama’a ke yi kan batun ɗauke wani ɓangare na Babban Bankin Nijeriya CBN zuwa Legas da kuma kamfanin FAAN inda ya ce akwai buƙatar gwamnati ta fito da hanyoyi na fihimtar da mutane kan waɗannan lamura.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *