Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

0
39
Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Sarkin Gwandu ya naɗa ɗan Buran ɗin Gwandu babba

Daga Haruna Abdulrashid

Shugaban majalisar sarakuna ta jihar Kebbi, Mai martaba Sarkin Gwandu, Manjo-Janar Muhammadu Ilyasu Bashar Mni, ya karrama Shugaban hukumar jin daɗi da walwalar Alhazzai ta ƙasa, Malam Jalal Muhammad Arabi da sarautar (ƊAN BURAN GWANDU BABBA) inda mai martaba sarki ya aike da tawaga zuwa birnin tarayya Abuja domin gabatar da wannan karramawa zuwa ga Malam Jalal Arabi.

Da ya ke jawabi a madadin mai martaba sarkin Gwandu Alhaji Aminu Ahmad, Sarkin Fadan Gwandu ya bayyana cewa mai martaba sarkin Gwandu ya amince da bayar da wannan karramawa ga Malam Jalal ne a bisa jajircewa da kuma taimako da yake yiwa Alhazzan Najeriya tare da haɗin kai da yake bawa shugabanni a kan abin da ya shafi harkar aikin Hajji mussaman a bana.

Shi ma shugaban hukumar jin daɗin da walwalar Alhazai ta jihar Kebbi, Alhaji Faruƙu Musa Yaro Enabo, Jagaban Gwandu, ya bayyana jin daɗin shi matuƙa a kan wannan karramawar da aka yi wa maigidan shi.

Ya kuma yabawa mai martaba Sarkin Gwandu Manjo-Janar Muhammadu Ilyasu Bashar akan yadda yake gabatar da kyakkyawan jagoranci zuwa ga Al’ummar Gwandu.

Wannan bayar da takardar karramawa ta sarautar (ƊAN BURAN GWANDU) Sun haɗa da Alh Aminu Ahmed Sarkin Fadan Gwandu, Alh Aminu Abubakar Gulumbe Uban ƙasar Gulumbe, Alh. Mustapha Ka’oje Sarkin Bargun Ka’oje, Alh Lamiru Shehu Sakataren Sarakunan jihar Kebbi, Alh Faruƙu Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu, Alh Usman Osho da Alh Rilwanu Awwal.

Mai girma Shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi, Malam Jalal Arabi, ya bayyana jin daɗin shi sosai ganin wanan karramawa da ya samu daga masarautar Gwandu.

Ya kuma ce jihar Kebbi ta zama gida a gareshi ganin yadda yake samun karramawa da mutuntawa a jihar ya kuma bayyana mana irin mutunci da zumunci dake tsakanin shi da shugaban hukumar Jin daɗi da walwalar Alhazzai ta jihar Kebbi.

Alh Faruku Musa Yaro Enabo Jagaban Gwandu ya kuma yi godiya da jinjina zuwa ga Maigirma Gwamnan jihar Kebbi His Excellency Comrd Dr. Nasir Idris Ƙauran Gwandu akan irin yadda yayi ɗawainiya ga Alhazzan jihar shi.